Wani matashi mai shekara 29, Akarachi Amadi, ya doke dan majalisa mai ci a karashen zaben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Mbaitoli/Ikeduru da ke Jihar Imo, Honorabul Henry Nwawuba.
Akarachi Amadi wanda shi ne dan takarar Jam’iyyar APC ya yi nasara ne a zaben da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta karasa a ranar Asabar.
- Yadda jam’iyyu suka kacaccala kujerun sanatoci a Zaben 2023
- INEC za ta yi taron gaggawa kan zaben Adamawa
Da farko dan takara Jam’iyyar LP, Uche Ogbuagu ne ka kan gaba a lokacin da aka fara zaben a ranar 25 ga watan Fabrairu, amma a karshe Akarachi ya yi masa fintinkau.
Baturen zaben, Farfesa Boniface Okoro, ya ce matashin ya lashe zaben ne da kuri’u 21,372 a yayin da Uche Ogbuagu na jam’iyyar LP ya zo na biyu da kuri’u 18,296.
Dan majalisa mai ci, Henry Nwawuba na Jam’iyyar APGA shi ne ya zo na uku da kuri’u 7,202, a yayin da dan takarar PDP, Usmond Ukanacho, ya samu kuri’u 6,681.
Chinonso Uba na ADC ya samu kuri’u 4,100, a yayin da Godstime Chukwunuikem na SDP ya tashi da kuri’u 246.
Da take tabbatar da hakan, kakakin INEC ta Jihar Imo, Dokta Chinenye Chijioke Osuji, ta kara da cewa a zaben dan majalisar dokokin jihar, PDP ta ci kujera daya, ta mazabar Isu wadda Modestus Osakwe na PDP ya lashe.
Reshen jam’iyyar PDP na jihar ta bayyana nasarar da ta samu a zaben majalisar jihar babbar nasara ce.