Sakamakon share fagen zaben shugaban kasar Kenya na nuna cewa manyan ’yan takara biyu da ke fafutukar ganin sun gaji shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, na tafiya kafada-da-kafada.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa, zaben na ranar Talata ya kasance wani muhimmin gwaji kan samun daidaito a kasar mafi girman tattalin arziki a Gabashin Afirka, bayan zabuka uku da suka gabata cikin takaddama da zargin magudi.
- An sako mutum 6 ’yan gida daya cikin fasinjojin jirgin kasan Kaduna
- Tabarbarewar Tsaro: Gombe Ta Kafa Rundunar ‘Operation Hattara’
’Yan takarar da ke kan gaba dai su ne mataimakin shugaban kasar William Ruto, da kuma madugun ’yan adawa Raila Odinga.
Sakamakon da gidan talabijin mai zaman kansa na kasar ya bayyana a safiyar Laraba, na nuna kowannen suna da kusan kashi 49 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
A dokar kasar dai dole ne dan takara ya samu kashi 50 da karin kuri’a daya, kafin bayyana shi a mtsayain wanda yayi nasara.
Hukumar zaben kasar ta fitar da hotunan sama da kashi 90 cikin 100 na sakamakon zaben daga rumfunan zabe 46,663.
Daga yanzu dai hotuna kawai hukumar ta ce za ta dinga wallafawa, ba adadin kuri’un ba.
A dokar kasar da wajibi ne a kai sakamakon zaben cibiyar kirga kuri’u ta kasa da ke babban birnin kasar, Nairobi, sannan a tantance kafin hukumar ta fitar da su a matsayin sakamako.
Ana sa ran sakamakon karshe daga hukumar ya fito nan dawasu kwanaki, duk da a dokance sai ya kai mako guda.