Hukumar Zaben kasar Kenya a ranar Litinin ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar da aka yi makon jiya.
Gabanin sanar da sakamakon dai, Kwamishinonin zabe hudu sun ki amincewa da kidayarsa.
- An karrama dan sandan da ya ki karbar cin hancin $200,000 a Kano
- ’Yan bindiga sun kashe malami a makarantar sakandaren jihar Nasarawa
“Wanna nasara ta samu ne saboda mutanen Kenya su daga martabar siyasar kasar,” in ji zababben shugaban kasar bayan sanarwar.
Yanzu mun bawa baya baya, lokaci ne kuma da za mu fuskanci gaba. Kuma domin hakan muna bukatar hadin kan kowa.”
Shugaban hukumar ta IEBC ya bayyana cewa Ruto ya samu kashi 50.49 na kuri’un da aka kada, yayin da Odinga ya samu kashi 48.85.
Rikici dai ya kunno kai gabanin sanar da sakamakon, bayan da mataimakin shugaban hukumar zaben da wasu kwamishinonin uku suka shaida wa manema labarai cewa ba za su iya goyon bayan rashin tabbas din matakin tatttara sakamakon zaben na karshe ba.
An da fice da jami’an diflomasiyya da zabukan kasa da kasa daga zauren kirga kuri’un kafin Chebukati ya tsawatar.
Yayin da ake fargabar cewa zarge-zargen magudin zabe na iya haifar da zubar da jini kamar yadda ya faru a zaben 2007 da 2017, Cherera ya bukaci bangarorin da su warware duk wata takaddama a kotu.
Wannan dai mataki ne na dakile makamantan zarge-zargen magudin da ya haifar da tashin hankali a zabukan 2007, da ya haddasa mutuwar fiye da mutane 1,200.