✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin haraji: Shugaban Kenya ya janye kudirinsa

Shugaban Kenya ya janye kudirinsa bayan zanga-zangar da aka rasa rayuka

Shugaban Kenya William Ruto ya janye kudirinsa na ƙarin kuɗin harajin da yake shirin yi, bayan matsin lambar da ya sha daga masu zanga-zangar da suka kutsa kai cikin zauren Majalisar Dokokin Ƙasar, tare da yin barazanar ci gaba da ɗaukar ƙarin wasu matakai na nuna adawa da shirin, muddin shugaban ya yi gaban kansa wajen sanya wa dokar hannu.

A wani jawabi da ya gabatar a kafar talabijin, shugaba Ruto ya ce ba zai rattaba hannu kan kudirin dokar da ke tattare da ƙarin kuɗin harajin ba, matakin da ke nuna cewa ya bada kai bori ya hau.

A ranar Talata ce aka yi wata mummunar arangama tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga a Majalisar Dokokin Ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 23 tare da jikkata wasu dama kamar yadda Ma’aikatan Lafiyar Ƙasar suka bayyana.

Shugaban ya ce a yanzu zai fara tattaunawa da matasan ƙasar da ke jagorantar zanga-zangar don warware matsalolin da ke tsakaninsu, inda zai fara da daukar matakin rage kasafin kudin fadar shugaban ƙasar.

Wannan matakin ana ganin sa a matsayin wata gagarumar nasara, da wannan zanga-zangar da ta samo asali daga kafofin sada zumunta kuma aka kwashe tsawon mako guda ana yi ta samu.

To sai dai duk da daukar wancan mataki da shugaba Ruto ya yi, daya daga cikin jagororin zanga-zangar Hanifa Adan, ya bayyana matakin a matsayin bam-ba ɗanci, domin a cewarsa shugaban ba zai iya dawo da rayukan waɗanda suka rasu ba.

Take hakkin bil’adama

Wannan al’amari ya sa hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasar ke neman a bi bahasin waɗannan aka kashe, domin shugaban ya fuskanci laifin take hakkin bil’adama.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren abin da shugaban hukumar David Malombe ke cewa.