Shugaban Kasar Kenya, Willam Ruto ya dakatar da jami’an hukumar zaben kasar (IEBC) su hudu, wadanda suka ja da sanarwar zaben da ya lashe a watan Agusta.
Matakin Shugaban ya fito fili a ranar Juma’a bayan da Majalisar Kasar ta bukaci William Ruto ya kafa kwamitin da zai binciki Kwamishinonin zaben hudu kan matsayin da suka dauka bayan zaben.
- Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Mataimakin Shugaban Kenya
- Zaben Kenya: Dan takara ya yi harbi da bindiga a rumfar zabe
Jami’an hudu; Juliana Cherera da Justus Nyang’aya da Irene Masit da kuma Francis Wanderi sun nuna rashin gamsuwar su da lissafin kidayar kuri’ar da aka jefa, da cewa da akwai aringizo a ciki.
Ruto ya samu nasara da kaso 50.49 na jimlar kuri’un da aka kada yayin da abokin takararsa, Raila Odinga ya samu kaso 48.85 a zaben.
Odinga ya kira matakin Ruto da cewa wani shiri ne na tafka magudi a zaben shekarar 2027 da ke tafe.
“Abin a bayyane ya ke, Ruto ya soma kulle-kullen tafka magudi a zaben 2027 tun a shekarar 2022. Ba kuma zamu yarda hakan ta faru ba” in ji Odinga.
Jami’an hudu sun kira taron ‘yan jarida ne a inda suka bayyana matsayinsu na kin amincewa da sakamakon zaben, jim kadan bayan shugaban hukumar zaben ya sanar da nasarar ta Ruto.