Rahotanni daga kasar Kenya na nuni da cewa masu aikin ceto na ci gaba da laluben gano akalla mutum 10 da suka makale a buraguzan wani benen da ya rushe a Nairobi, babban birnin kasar.
An ce galibin wadanda lamarin ya shafa leburorin da ke aiki ne a wajen gina benen mai hawa bakwai.
- Poland ta zargi Rasha da harba mata makami mai linzami
- Sojoji sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram da wasu mayaka 14 a Borno
Iftila’in rushewar ginin ya faru ne a ranar Talata da tsakar rana a yankin Kasarani na kasar.
Rahotanni sun ce sau biyu jami’i mai sanya ido kan aikin ginin yana yin watsi da gargadin hukumomi kan a dakatar da aikin ginin duba da rashin ingancin aiki.
Har zuwa safiyar ranar Laraba, an ga tawagar masu aikin ba da agajin gaggawa na ci gaba da kokarin gano wadanda ake kyautata zaton suna nan makale a karkashin buraguzan ginin.