Mutane hudu sun jikkata sakamakon rushewar gini a yankin Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.
Rushewar ginin ya auku ne a kusa da Kwalejin Gwamnati da ke garin Riyom safiyar Litinin, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Wani mazaunin garin, Dusu Joseph, ya ce “Ba a samu asarar rai ba, amma yawancin waɗanda suka samu rauni ƙananan yara ne kuma an kai su asibiti domin duba lafiyarsu.”
Shi kuma wani mai suna Bot Rwang, godiya ga Allah ya yi bisa yadda iyalan da ke cikin gidan da ya ruguje suka tsallake rijiya da baya, babu asarar rai.