Kotun Majistare Mai lamba 5 da ke Gidan Murtala ta fara sauraren shari’ar matar nan da ake zargi da kashe ’ya’yanta biyu a Unguwar Sagagi a cikin birnin Kano.
A watan Oktoba ne ’yan sandan Gwale suka kama matar mai kimanin shekara 26 da haihuwa bisa tuhumarta da amfani da adda ta kashe ’ya’yanta guda biyu; Irfan Ibrahim dan kimanin shekara shida da kanwarsa Fatima Zuhura ’yar kimanin shekara uku, tare da raunata kanwarta mai suna Aisha Abdullahi ’yar shekara goma da haihuwa.
- ’Yan Kasuwar Kantin Kwari sun koka kan dokar Ganduje
- Yadda aka yi jana’izar mahaifin Kwankwaso a Kano
A zaman kotun, Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Lamido Abba Sorondinki ya karanta wa wacce ake kara tuhumar kisan kai ga ’ya’yanta ga kuma munanan raunika da ta yi musu wanda ya ce laifi ne da ya sava da sashe na 221 da 245 na Kundin Penal Code.
Sai dai a martaninta Hauwa Habib ta musanta hakan inda ta ce ita ba ta san abin da ya faru ba domin haka a saninta ba ta yi wa ’ya’yanta komai ba, haka su ma ba su yi mata komai ba.
Sai dai lauyar da ke kare wacce ake kara Barista Huwaila Ibrahim ta roki kotun da ta bayar da umarnin mayar da wacce ake zargi zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano don kula da lafiyarta.
Shi ma Lauyan Gwamnatin ya roki a damka wacce ake tuhuma ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano a maimakon mayar da ita
gidan yari.
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Hauwa Minjibir ta amince da rokon duka lauyayin guda biyu inda kuma ta dage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Janairu, 2021.