✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara shari’ar masu hannu a  batun Zainab Aliyu

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fara sauraren kara game da zargin da ake wa wadansu mutum shida da sanya wa Zainaba Aliyu kwaya…

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fara sauraren kara game da zargin da ake wa wadansu mutum shida da sanya wa Zainaba Aliyu kwaya a jakarta lamarin da ya janyo kasar Saudiyya ta tsare ta na tsawon watanni kafin daga a sake ta.

Idan za a iya tunawa tun a watan Disamban bara ne Zainab Aliyu Habibu ta tafi Saudiyya don yin aikin Umara tare da mahaifiyarta da yayarta inda wadanda ake zargin suka yi amfani da wannan dama suka sanya wata jaka mai dauke da kwaya da kuma sunansa  a jirgin da ya kai su Saudiyya.

Bayan su Zainab sun sauka a Saudiyya da kwana biyu ne aka kama ta aka kai ta gidan kurkuku a wani mataki na zaman jiran shari’a.

Wadanda ake zargin wadanda ma’aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano sun hada  da Umar Shehu da Umar Sanda da Sani Sulaiman da Nuhu Adamu da Raudha Adediji Uduson Oweh da Sani Hamisu.

A zaman kotun lauyan Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Femi Olaritumba ya gabatar da shaidu biyu ciki har da matar da ta shirya wa wadanda ake zargi tafiyar inda ta shaida wa kotu cewa ta bayar da takardun shaidar tafiyarsu guda uku da kuma jakunkunansu guda uku. Amma a cewarta ba ta san yadda aka gano wancan jakar mai dauke da kwaya ba.

Alkalin Kotun Mai shari’a Luwes Alagoa ya dage sauararen karar zuwa ranar 21 da kuma 22 ga Oktoba don ci gaba da sauraren shaidu.