✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara rububin dan kwallon Eaglets Osimhen a Ingila

Raotanni da ke fitowa sun nuna kulob din Manchester City da Chelsea da kuma na Liberpool da ke Ingila ne suka fara rububin dan kwallon…

Raotanni da ke fitowa sun nuna kulob din Manchester City da Chelsea da kuma na Liberpool da ke Ingila ne suka fara rububin dan kwallon Golden Eaglets bictor Osimhen don ganin sun dauke shi da zarar an kammala gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da yanzu haka ke gudana a Chile.

Ya zuwa jiya Alhamis (kafin wasan Najeriya da Meziko) Osimhen ne yake kan gaba wajen zura kwallaye a raga bayan ya zura kwallaye 8.
Osimhen dan kimanin shekara 17, an shaide shi ne wajen iya zura kwallo a raga da zarar ya samu dama. Hasalima dan kwallon ne ya zama zakara wajen zura kwallo a gasar cin kofin matasa na Afirka (U-17) da ya gudana a Nijar a wannan shekara bayan ya zura kwallaye hudu da hakan ta sa zarce kowane dan kwallo a gasar.
Rahoton ya nuna daya daga cikin kulob din da ke zawarcinsa ya taya dan kwallon a kan Fam miliyan 1 inda ya gabatar da tayin ga kulob din da Osimhen ke yi wa kwallo a Najeriya watau Ultimate Strikers Academy. Idan cinikin ya kaya, akwai yiwuwar dan kwallon ya koma Ingila da zarar an kammala gasar cin kofin duniya na matasa da ke gudana a Chile.
Idan za a tuna wasu daga cikin ’yan kwallon Golden Eaglets da suka samu nasarar lashe kofin a shekarar 2013 da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun samu kulob a Ingila. Kulob din Manchester City ne ya dauke Kelechi Iheanacho yayin da kulob din Tottenham kuma ya dauke Chidebere Nwakali da Musa Yahaya.