Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayayyakin adana amfanin gona ga manoma a Jihohi 19 da ke fadin kasar nan domin magance barazanar karancin abinci.
Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona ta Kasa, Dokta Ernest Umakhihe, shi ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake kaddamar da rabon kayan ga manoma a ranar Laraba.
- An kashe kwamandan ’yan banga a artabu da ’yan bindiga
- An dakatar da Sakataren Hukumar alhazan Bauchi
Ya ce bai wa manoman kayayyaki zai ba su damar alkinta amfanin gonarsu, sakamakon yadda mafi yawa daga cikin manoma suke asarar amfanin gona a dalilin rashin kyakkyawan wajen ajiya tun daga gona zuwa gida.
Umakhihe, ya kuma tabbatar da cewa shirin zai taimaka wajen kawo wadatar abinci a kasa da kuma farfado da tattalin arziki.
Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta gano bakin zaren matsalar killace amfanin gona yadda ya kamata, wanda shi ne musababin asara mai tarin yawa ga manoma.
Kazalika, ya ce ba wa manoma tallafi da kuma samar musu da yanayin da za su kilkace amafanin gonar da suka girbe zai ba su kwarin gwiwa wajen rage asarar da suke tafkawa.