Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya (NRC, Gundumar Arewa maso Gabas ta kaddamar da shirin daukar fasinjoji a garin Bauchi, inda za a rika jigilar fasinjojin daga Tashar Reliwai zuwa kauyen Inkil da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.
Malam Aliyu Mainasara, Manaja Mai kula da yankin ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin daukar fasinjojin a garin Bauchi.
- Bene mai hawa 7 ya danne mutane a Legas
- Mutum miliyan 30 za su rasa aikin yi idan aka hana acaba a Najeriya – Musa Maitakobi
Malama Mainasara ya ce, za a rika yin jigilar ce daga ranar Litinin zuwa Asabar sau uku a rana, inda za a rika biyan Naira 200 .
A cewarsa, kowace jigila za ta kasance tare da jami’an tsaro domin kare fasinjoji da dukiyoyinsu.
“Jirgin zai iya yin jigilar fasinjoji kusan 70 zuwa 100,” inji shi.
Ya ce, cikakken aikin zai fara ne ranar Litinin mai zuwa 5 ga Satumba, 2022, inda ya bayar da jadawalin jigilar yau da kullum da kuma wata-wata.
Ya ce, a yankin na Arewa maso Gabas an dade ba a gudanar da harkar sufurin jirgin kasa ba, saboda rashin tsaro da lalata hanyar jirgin.
“Shirin zai bai wa ’yan kasa da yara damar sanin yadda jirgin kasa yake, saboda akwai mutane da dama da ba su san jirgin kasa ba. Wannan wata dama ce ga yaran da suke makarantu, inda za su je yawon shakatawa daga Tashar Bauchi zuwa Unguwar Inkil mai tazarar kilomita biyar,” inji shi.
Malam Mainasara ya ce, suna fata nan da karshen bana za su kara sufurin jirgin zuwa karamar Hukumar Alkaleri zuwa Jihar Gombe.
Ya ce, injiniyoyi a gundumar suna aiki kan yadda za a fadada zirga-zirgar har zuwa karamar Hukumar Alkaleri.
“Lokacin da aka kammala aikin gyara hanyoyin zuwa Alkaleri, za mu fara gudanar da zirga-zirgar har zuwa garin Gombe.
Sai ya bukaci masu ruwa-datsaki su tallafa wa shirin ofishin Gundumar Arewa maso Gabas na hukumar da sahihan bayanai don tabbatar da sa-ido da kare layukan dogon.