✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gyaran titin jirgin kasan da aka dasa wa bam a hanyar Kaduna

An girke jami’an tsaro da dama don gadin masu aikin gyaran titin

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin girke jami’an tsaro a daidai wajen da aka dasa bam a titin jirgin kasa, yayin da aka fara aikin gyaran shi.

Baya ga jami’an ’yan sandan da aka jibge a wajen, an kuma kawo dakarun sojoji domin gadin da ma’aikatan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) da ke aikin gyaran titin da kuma taragan jirgin.

An dai debo ’yan sandan ne da sassa daban-daban na rundunar.

Mai rikon mukamin kakakin rundunar, ta kasa, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar, ya ce jami’an tsaron za su rika sintiri a tsawon kilomita 163 na titin Abuja zuwa Kaduna domin tabbatar da tsaro.

Ya ce Babban Sufeton ya taka har wurin da aka dasa bam din da kafarsa inda ya shaida girke jami’an da kuma karfafa wa matafiya gwiwa.

Ya ce bayan jibge ’yan sandan, yanzu ana iya cewa komai ya koma daidai a kan babbar hanyar, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da ba su bayanan sirri don dakile matsalar baki daya.