✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar damben Kofin Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta nanata aniyarta ta  bunkasa harkar wasannin gargajiya a fadin jihar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka lokacin bikin bude…

Gwamnatin Jihar Kano ta nanata aniyarta ta  bunkasa harkar wasannin gargajiya a fadin jihar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka lokacin bikin bude gasar dambe ta cin Kofin Ganduje wanda aka yi wa take da ‘Ganduje Dambe International 2019’.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare a Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jihar, Alhaji Ibrahim Ahmad Sagagi ya bayyana cewa an shirya gudanar da gasar ce da nufin bunkasa harkar al’adun gargajiya na Hausawa a jihar da kasa baki daya.

Gwamnan ya yi alkawarin  gwamnati za ta ci gaba da bayar da duk taimakon da ya kamata wajen bunkasa gasar damben gargajiya a jihar inda ya kara da cewa akwai bukatar masu ruwa-da-tsaki su sanya hannu wajen bunkasa harkar wasanni a jihar.  “Hakan shi zai sanya masu zuba jari su sanya dukiyarsu a wannan jaririyar ma’aikatar ta matasa da wasanni  tare da tallafa wa matasa su zama masu dogaro da kansu,” inji shi.

Da yake jawabi Shugaban Kungiyar ’Damben Gargajiya ta Jihar Kano, Alhaji Mamman Bashir Danliti  ya bayyana jin dadinsa ga wannan gasa ganin cewa za ta sama wa matasa aiki don a dama da su cikin harkar wasannin gargajiya.

A wannan rana  ’yan wasan damben sun fafata da junansu inda a zagayen farko Dogon Sharif ya doke abokin karawarsa Shamsun Tarara. Haka kuma Garkuwan Chindo ya doke abokin karawarsa Bahagon Mancha. Yayin da Horon Kande ya doke Champion.

A zagaye na biyu kuma an fafata  ne tsakanin  Balan Gada da Garkuwan Gawuna sai kuma Dogon Aleka inda ya doke Dangidan Yawale. Sai kuma Shagon Danbature da ya ci nasara a kan Dan Hausa.

A yanzu haka dai ana ci gaba da fafatawa a tsakanin ’yan wasan inda aka shiga rana ta uku.