An fara buga gasar kwallon kafa ta cin kofin Kwamared Sunusi Sufwan Saminaka (Kofin Sunusiyya) na bana a babban filin wasa na garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, a ranar Litinin da ta gabata.
Kungiyoyin kwallon kafa 16 ne daga mazabun Karamar Hukumar Lere 11 za su fafata a gasar.
A wajen bude gasar Mazabar ’Yar Kasuwa da Kayarda ne suka fara fafata, inda aka tashi wasan da ci 1-1.
Da yake zantawa da wakilinmu Kwamared Sunusi Sufwan Saminaka, ya ce ya fara sanya kofin ne a bara, domin kara dankon zumunci a tsakanin matasan Karamar Hukumar Lere baki daya.
Ya ce domin harkar wasan kwallon kafa a Najeriya da sauran harkokin wasanni abubuwa ne da suke kara dankon zumunci da nisantar da matasa daga aikata miyagun abubuwan da suke kawo rashin zaman lafiya.
Ya ce kowa ya san harkar kwallon kafa sana’a ce mai inganci, wadda idan Allah Ya taimaki mutum daga irin wadannan kananan gasa, zai iya kaiwa ko’ina a duniya. Saboda yawaicin manyan ’yan kwallo da irin wannan suka fara.
Kwamared Sunusi ya bada tabbacin cewa a karshen gasar, wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku, za a ba su kyaututtuka domin a karfafa musu gwiwa.
Bukin bude gasar, ya samu halartar manyan ’yan siyasa da dubban matasa daga kowane bangare na Karamar Hukumar Lere.