A farkon wannan makon ne kungiyar da ke sa ido kan kudaden yakin neman zabe na Kasar Faransa ta bayyana cewa Shugaban Kasa, Emmanuel Macron ya karbi tallafin yakin neman zabensa.
Masu shigar da karar sun kaddamar da wannan bincike ne don gano hanyoyin da aka bi tare da zuba makudan kudaden a yakin neman zaben shugaban kasan.
Wannan mataki dai ya biyo bayan wasu bayanan sirri da wata hukuma dake da nauyin sa ido dangane da yadda ake kashe kudaden yakin neman zabe ta bayar.
An dai bayyana cewa an zuba wadanan kudade ne tare da yin amfani da takardun bankuna. Masu bincike na kokarin gano ko masu taimakawa kungiyar ba su wuce adadin da aka kayyade na Yuro 7, 500.
To amma sai dai shugaban hadakar ’yan adawan kasar, Jean Luc Melenchon ya danganta wannan yunkuri da cewa siyasa ce kawai babu gaskiya cikin binciken.
Melenchon ya diga ayar tambaya, inda ya ce ’yan sanda zasu iya yin dirar mikiya a gidan Shugaban Kasar, ko kuma za su iya sanar da al’umma sunayen mutanen da suka ba da wadanan kudade?