✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara allurar rigakafin zazzabin cizon sauro na farko a duniya a Kamaru

Wata yarinya mai wata takwas a duniya ce dai aka fara yi wa allurar rigakafin

An fara yi wa kananan yara allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko a duniya, mai suna RTS,S a kasar Kamaru.

Wata yarinya mai wata takwas a duniya ce dai aka fara yi wa allurar rigakafin a wata cibiyar kiwon lafiya da ke kusa da birnin Yaoundé ranar Litinin.

Kaddamar da allurar rigakafin zazzabin cizon sauro na daga cikin matakan da hukumomi suka dauka domin ceto rayukan dubban yara a fadin Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar cewa a mutum 600,000 ne ke mutuwa a Afirka a duk shekara sakamakon zazzabin cizon sauro.

WHO ta ce a cikin wadanda ke mutuwa a sakamakon cutar, yara ’yan kasa da shekaru biyar su ne akalla kashi 80 cikin 100.

Ƙasar Kamaru tana ba da allurar rigakafin mai suna RTS,S kyauta ga duk jariran da suka kai watanni shida da haihuwa.

Jami’an lafiya sun ce za a ba da alluran ne a daidai lokacin da ake ba yaran sauran alluran rigakafin da aka saba ba su, domin saukaka wa iyaye zaryar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya.

Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta ta ce, wannan na zuwa ne bayan nasarar da aka samu a kasashen Kenya da Ghana da kuma Malawi — inda allurar ta rage mace-macen da cutar ke haddasawa da kashi 13 cikin 100 a yaran da suka kai shekarun da suka cancanta.

Masu bincike daga Amurka sun bayyana cewa allurar rigakafin na da tasirin da zai iya ceto akalla mutum daya a cikin duk yara ukun da aka yi wa ita.

WHO ta yaba da kaddamar da shirin a Kamaru a matsayin wani lokaci mai cike da tarihi a yakin da duniya ke yi da cutar zazzaɓin cizon sauro.

A shekara ta 2021, Afirka ce ke da kashi 95 cikin 100 na masu zazzabin cizon sauro a duniya da kuma kusan kashi 96 ciki 100 na mace-mace masu alaka da cutar.

WHO ta ce a duk shekara ’yan ƙasar Kamaru kusan miliyan shida ke kamuwa da cutar, inda mutum 4,000 ke mutuwa, akasarinsu yara ’yan kasa da shekaru biyar.

An shafe shekaru 30 ana gudanar da bincike domin samar daigakafin RTS,S, karkashin jagorancin kamfanin samar da magunguna na  GSK na Birtaniya.