✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun sace mutane 29 a Katsina

’Yan bindiga sama da 50 dauke da muggan makamai ne suka kai harin a Batsari da dare

’Yan bindiga sanye da kakin sojoji sun sace mutane 29 bayan a ƙauyen Tashar Na-Gulle da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sama da 50 dauke da muggan makamai ne suka mamaye kauyen ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Lahadi inda suka fatattaki mazauna ƙauyen.

Shaidu sun ce zuwan maharan kauyen ke da wuya suka fara harbul, sun shiga gidajen jama’a.

“Sun buƙaci mazauna yankin da kar su gudu, inda suka bayyana cewa su jami’an tsaro ne da aka tura domin su taimaka musu,” inji wani shaida.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Amma ya ce tuni aka dawo da zaman lafiya a yankin kuma ana ƙoƙarin ceto  waɗanda aka yi garkuwa da su.

A cewarsa, nan gaba a lokacin da ya dace rundunar za ta sanar da halin da ake ciki.