An baiyana naira dubu dari uku(N300.000.00) a matsayin mafi karancin kudin ajiya ga maniyatan aikin hajji na 2018 a Jihar Katsina. Daraktan hukumar jin dadin alhazai na jahar, Alhaji Muhammad Abu Rimi ne ya baiyana haka a wani taron manema labarai da aka yi a ranar larabar nan a hedkwatar hukumar da ke cikin garin Katsina. Daraktan ya ce za a ci gaba da yin wannan ajiya tun daga watan Nuwamban 2017 har zuwa cikin watan Maris na shekarar 2018. Masu sha’awar yin wannan ajiya za su kai takadar shedar zuba kudinsu na banki tare da takardar shedar zama dan karamar hukuma da kuma faspo nasu a ofishin shiyya na hukumar mafi kusa da maniyacin. Sannan ya ja hankalin masu yin ajiyar da su sani cewa,hukuma ba zata karbi tsabar kudi daga maniyaci ba. Don haka kada su yarda su bayar da kudinsu ga kowa sai a banki."Duk kuma wanda ya bayar da kudinsa ga wani to ya yi don kansa babu ruwan hukuma". Alhaji Abu Rimi ya kara da cewa, ga wadanda suka taba yin aikin hajjin a cikin shekara biyar da suka wuce, kuma suna son komawa a badi, za su kara naira dubu dari da sittin da uku bayan baiyana adadin kudin aikin hajjin na 2018 baki dayansa da hukumar aikin hajji ta kasa.