✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An dawo da wutar lantarki awa biyu bayan janye yajin aikin Kungiyar Kwadago.

An dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna, kasa da awa biyu bayan janye yajin aikin Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) na kwana biyar a Jihar.

Duk da dawowar wutar da misalin karfe 9.50 na daren ranar Laraba, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce bai ga alamar NLC ta janye yajin aikin da ya kira zagon kasa ga tattalin arziki da al’ummar jihar ba.

“Ba a dawo da wuta ba tun da aka dauke a ranar Lahadi, 16 ga Mayu, 2021 ta haramtacciyar hanya sabanin dokar kare muhimman ayyuka,” inji shi.

El-Rufai ta bakin kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya jaddada muhimmancin dawo da wutar yana mai gargadin NLC cewa ta kwana da sanin cewa ba batu ne na sharadi ko tattaunawa ba.

“Gwamnatin Kaduna ba za ta yi wata tattaunawa ba, matukar aka hana jama’a samun wutar lantarki.”

Ya ce yanke wutar lantarkin da aka yi a ranar Lahadin ne ya sa gwamnatinsa ta janye batun tattaunawa da NLC a ranar.

“Dauke wutar awa 18 kafin lokacin da suka sanar tamkar tare gwamnati da bindiga ne, kuma ba za mu lamunci zagon kasa ba,” inji shi.

Dawowar wutar ta sanya farin ciki a zukatan mutanen Kaduna wadanda rabonsu da ita tun ranar Lahadi da sanyin safiya.