Mahukuntan sun kafa sabuwar doka da za ta hana zance a tsakanin samari da ’yan mata da zawarawa a Karamar Hukumar Rano da ke Jihar Kano.
Mahukuntan sun ce sun sanya dokar ce tsakanin masu neman aure a fadin karamar hukumar da zummar kawo tsafta tsakanin samari da ’yan mata da ma zawarawa.
Wata sanarwa da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Dahiru Muhammed Ruwan Kanya, ya fitar ta ce an dauki matakin ne ganin yadda ake lalata ’yan mata da sunan neman aure.
Shugaban Karamar Hukumar, ya ce lalacewar tarbiyya ce dalilin kafa dokar, don haka ya zama tilas su tabbatar da kyakkyawar tarbiyya a tsakanin matasa da zawarawan yankin.
Ya kara da cewar, daga yanzu iyaye da sauran al’ummar gari za su tabbatar ana zance bisa tsarin da aka shimfida.
Kazalika, ya ce hukumar Hisbah da sauran masu ruwa da tsaki a Rano da suka hada da limamai da manyan gari za su tabbatar da dorewar dokar.
Sannan ya kara da cewa jami’ai za su rika gudanar da sintiri domin tabbatar da cewa ba a samu masu kunnen kashi da za su yi fatali da dokar ba.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka kafa irin wannan doka a jihar Kano ba.
Ko a watannin da suka shude mahukunta a unguwar Tudun Yola da ke Birin Kano sun kafa dokar hana zance a tsakanin samari da ’yan mata da dare.