Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Katsina ta sanar da dawo da dokar hana hawa babur daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6:00 na safe a birnin Katsina saboda matsalar tsaro.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya fitar a Katsina ranar Litinin.
- Jirgin farko dauke da hatsi ya bar Ukraine zuwa kasuwar duniya
- Ta’addanci: Daruruwan mutane sun tsere daga yankin Birnin-Gwari
Sanarwar ta ce, “An umarce ni da in jawo hankalin jama’a cewa haramcin hawa babur a birnin Katsina daga karfe 10 na dare zuwa 6:00 na safe ta dawo,” inji sanarwar.
Tun a cikin watan Azumi ne dai rundunar ta sanar da dage haramcin domin bayar da dama ga jama’a su gudanar da harkokin ibadarsu.
Sake maido da dokar ya biyo bayan samun yawaitar kai hare haren da ake samu daga ‘yan bindigar da ke amfani da babura a wajen kai hare haren a yankunan kananan hukumomin da ke fuskantar wannan matsalar.
Sai dai sabon matakin a sauran kananan hukumomi, musamman wadanda ke fama da rikici har yanzu dokar tana nan daram.