✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan…

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali.

“An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa.

“Daga shekaru uku baya zuwa yanzu a hankali zaman lafiya ya fara dawowa Borno, amma lamarin ya sauya a ‘yan kwanakin nan,” in ji shi

Zulum ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura jiragen yaƙi masu saukar ungulu, da sabbin jirage marasa matuka da aka saya domin tallafawa ayyukan soja a wuraren da abin ya shafa.

“Duk da muna yaba wa sojojin Najeriya, ‘yan sanda, da jami’an DSS kan kiyaye doka da oda a Borno, dole ne mu kuma faɗi gaskiya, in ba haka ba, duk nasarorin da muka samu ya zuwa yanzu za su zama na banza,” in ji shi

Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jajirce waje. Tabbatar da yankin arewa maso gabashin kasar ya samu kulawar da ta kamata.

“Hankalin sojojin Najeriya da ma’aikatar tsaro ba akan jihohin arewa maso gabas yake ba, la’akari da halin da yankin ke ciki, mun cancanci samun kulawar da muke kira a ba mu.

“Yankin Sahel yana da matukar muhimmanci, kuma Borno ta yi iyaka da Jamhuriyar Chadi, Nijar da Kamaru.

“Yawancin ‘yan kasashen na shigowa Najeriya ne ta Borno, don haka idan ba a yi abinda ya kamata ba, jihar za ta sake shiga cikin rikici.