Wata kotun gargajiya ta yanke wa ’yan acaba 29 hukuncin daurin shekara uku kowannesu, kan saba dokar haramta sana’arsu a Zariya, jihar Kaduna.
Mai shari’a Madam Keziah Isaac Austin, wadda ta ce dukan wadanda aka samu da laifin sun amsa laifin ta ba su zabin biyan tarar N10,000 ko zaman gidan yari.
- Dokar Cire Kudi: Emefiele Ya Wuce Gona Da Iri —Dan Majalisa
- Karancin Mai: DSS Ta Ba NNPC Da IPMAN Wa’adin Sa’a 48
Tun da farko dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa an kama ’yan acabar ne a wurare daban-daban a yankin Dan Magaji a Wusasa Zariya a ranakun 3 da 5 ga watan Disamba 2022.
Yunusa ya ce an kama su ne a yayin da suke gudanar da sana’arsu ta haya da babura, wadda ta saba wa dokar Jihar Kaduna ta hana haya da kuma hawa babura.