✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ta a kurkuku kan sayar da sabbin kudade

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta daure matar aure wata 6 da tarar N50,000 saboda sayar da sabbin takardun Naira.

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta daure matar aure wata 6 da tarar N50,000 saboda sayar da sabbin takardun Naira.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) ce ta gurfanar da matar auren bisa laifin hadahadar sababbin takardun kudin Naira da yawansu ya kai N897,900.00 da take sayarwa a bainar jama’a.

Hukumar ta ce a ranar Alhamis ne ta gurfanar da matar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas wadda ta yanke mata hukuncin daurin wata shida da tarar Naira naira dubu 50.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Chukwuekwu Aneke, ya bayar da umarnin cewa jimlar kudi N897,900.00 da wannan mata ta baje kolinsu a lokacin da aka kama ta sun zama mallakar Gwamnatin Tarayya.

Tun da farko sai da mai gabatar da kara, C.C.Okezei, ya kira jami’in hukumar EFCC mai suna Olagunju Abdul Malik, domin yi wa Kotun bayani a matsayin shaida a kan tuhumar da ake yi wa wannan mata.

Cikin bayaninsa, Abdul Malik, ya shaida wa kotun cewa bayan samun labarin sirri, sun kama Bilikis Adeyinka a ranar 27/04/2024 a lokacin da ta baje kolin sababbin takardun kudin Naira 897,900.00 nau’i daban-daban tana sayarwa a dandalin 10 Degree Event Center a kan hanyar Billings da ke Ikeja a Legas.

Sanarwar ta ce wannan mata ba ta musanta laifin da aka tuhume ta da aikatawa ba.