An gurfanar da wadansu matasa masu suna Umar Ya’u mai kimanin shekara 29 da ke Unguwar Tudun Maliki da Muhammed Shehu da ke Unguwar Gidan Zoo a gaban Kotun Majistare ta 47 da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano bisa zarginsu da hadin baki da yin sata.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Sanusi Muhammad ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Ya’u Isyaku ne ya kai kara ofishin ’yan sandan cewa wata rana mai karar ya je na’urar fitar da kudi a banki (ATM) na Bankin Access da ke cikin Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano domin ya cire kudi, amma sai aka yi rashin sa’a katinsa ya makale a cikin na’urar inda ya nemi taimakon Umar Ya’u domin ya fitar masa da katin. Ya ce bayan Umar ya ciro masa katin lokacin da yake mika masa katin sai ya musaya masa da wani katin na jabu.
Ya ce “A wannan rana Umar Ya’u da taimakon Muhammed Shehu ka je wata na’urar ATM ta daban ka cire Naira dubu 100 daga asusun ajiyar mai katin da ka musanya sannan a wannan dare ka sake cire Naira dubu 35 ka tura zuwa wani asusun ajiya a bankin First Bank mai lamba 3104505222 mallakar wata mai suna Binta Adam Yusuf, inda mai kudin ya samu sakon fitar da Naira dubu 135.”
Mai gabatar da karara ya ce “Daga nan ne mai kara ya je kotu ya samu takada aka kai bankin Fist Bank domin rufe wancan asusun ajiya da aka aike wa kudinsa ciki. A wannan lokaci ne aka samu mai asusun inda ta bayyana cewa ba ta san wadanda ake zargin ba, ta ce kasancewarta mai sana’ar abinci bayan sun ci abinci sai suka gaya mata ba su da kudi a hannu sai dai su biya ta kudinta Naira dubu biyar ta asusun ajiyarta inda ta ba su lambar asusunta suka aike mata da Naira dubu 35, ita kuma ta sa katinta na ATM ta fitar da wannan kudi, a cewarta a nan ta dauki Naira dubu biyar ta ba su sauran kudinsu.”
Dukan wadanda ake zargin sun amsa laifuffukan da ake zarginsu da su na hadin baki da yin sata wadanda suka saba wa sashe na 97 da na 286 na Kundin Shari’a na Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Huda H. Abdu ta yanke musu hukunci biyan tarar Naira dubu goma-goma ko su yi zaman kurkuku na wata bakwai-bakwai a matsayin laifin hadin baki, sannan za su biya Naira dubu ashirin-ashirin ko ku yi zaman kurkuku na shekara dai-dai a matsayin laifi na biyu. Sannan su biya mai kara kudinsa Naira dubu 135 ko kuma su yi zaman kurkuku na shekara bibbiyu.