✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An daure Mubarak Bala shekara 24 kan aikata sabo

Ya amsa dukkan caji 18 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa.

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Sakateriyar Audu Bako da ke Jihar Kano ta yanke wa matashin nan da ake tuhuma da laifin aikata sabo, Mubarak Bala hukuncin cin sarka na shekaru 24.

Wannan dai ya biyo bayan amsa laifin da ake tuhumarsa da matashin ya yi yayin zaman kotun a ranar Talata.

Bayanai sun ce mai shari’a Farouk Lawan ya karanto wa Mubarak Bala caji 18 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo, inda duk ya amsa ba tare da wata gardama ba.

Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

Ya amsa dukkan caji 18 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Ganin haka sai lauyansa James Ibor ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nusar da shi kan tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa, amma Mubarak ya ce ya ji ya gani.

Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.

Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.

Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.

Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Kazalika, ya ce babu wanda ya yi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.

A kan haka ne mai shari’a Farouk Lawan ya yanke masa hukuncin dauri na shekaru 24.