✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure matashi a kan musun kwallon kafa

Wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-gyadi ta daure wani matashi shekara guda bisa samunsa da laifin yi wa wani abokinsa dukan kawo wuka…

Wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-gyadi ta daure wani matashi shekara guda bisa samunsa da laifin yi wa wani abokinsa dukan kawo wuka lamarin da ya ja masa raunuka.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Lawal ya shaida wa kotu cewa matashin mai suna Mustapha Isa ya yi amfani da adda ya yi ta saran abokinsa a kan musun kwallon kafa da ya kaure a tsakaninsu. Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kai tsaye. Alkalin kotun, Mai shari’a Kabir Ibrahim Imam ya yanke wa matashin hukuncin daurin shekara daya ko biyan tarar Naira dubu goma, kuma zai biya Naira dubu 50 a matsayin kudin magani.