✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure dan bindiga shekaru 21 a Kaduna

Kotun ta same shi da laifin mallakar bindiga kirar AK-47 da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Kotu ta yanke wa wani mai mai garkuwa da mutane hukuncin daursin shekaru 21 a gidan yari a Jihar Kaduna.

Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a GRA Zariya ta yanke wa Mohammed Kyauta Aminu mazaunin kauyen Pan Daudu a Karamar hukumar Igabi hukuncin ne a ranar Litinin.

Kotun ta same shi da laifin mallakar bindiga kirar AK-47 da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu.

Da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Rabi Salisu Oladoja ta ce kotu ta daure Mohammed ne a karkashin sashi na 45 na Penal Kod 2017 inda zai kwashe shekaru 21 a gidan gyara hali.