Wasu masoya a kasar Indiya sun dauki hayar jirgin sama don gudanar da bikin aurensu a wani yunkuri na kauce wa matakan kariya na cutar Coronavirus.
Mutum sama da 160 ne suka amsa goron gayyatar bikin auren da aka gudanar a sararin samaniya.
- Gwamnati ta sauya wa Kwalejin Afaka matsugunni
- Bata-gari sun yi yunkurin kone caji ofis a Legas
- An yanke wa dattijo lafiyayyar kafa aka bar mai ciwon
Wani dan kasar Indiya mai suna Donthu Ramesh (DonthuRamesh) ne, ya fara wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Donthu, ya bayyana cewa masoyan sun dauki shatar jirgin na tsawon awanni biyu don bikin auren nasu.
Masoyan wanda suka fito daga yankin Tamil Nadu, wanda yana daga cikin yankunan da COVID-19 ta yi tsauri, mahukunta sun sanya dokar da haramta taron mutune da suka haura hamsin.
Tuni Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Saman Indiya, ta fara bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.