✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dauki nauyin maganin wanda ya shekara 10 da ciwon kafa

Wani bawan Allah da yake gudanar da harkokin masana’antarsa a cikin garin Legas ya dauki nauyin biyan magani da kudin aikin kafar Alhaji Bashir Badamasi,…

Wani bawan Allah da yake gudanar da harkokin masana’antarsa a cikin garin Legas ya dauki nauyin biyan magani da kudin aikin kafar Alhaji Bashir Badamasi, wanda kimanin watanni biyu ke nan da Aminiya ta zanta da shi, bayan ya shafe shekaru 10 yana fama da matsanancin ciwon kafa.
Kamar yadda rahoton baya ya nuna, ciwon kafar ya same shi ne bayan da ya fadi a kwalbati ya karye a cinya, kana mota ta buge shi a wajen bayan da aka yi masa dauri; abin da ya sake uzzura ciwon har ya kai ga an bukaci Naira dubu 600 domin a yi masa aiki a kafar. A wannan lokacin ne ya mika kokon bararsa ga jama’a, kasancewar karfinsa ya gaza duk abin da yake da shi ya kare kuma Allah Ya yi wa matarsa da ke kula da ’ya’yansa rasuwa.
A cewar majinyacin, bawan Allahn day a dauki nauyin, ya karanta labarin halin da yake ciki a jaridar Aminiya sai ya ba da cigiyarsa. “Bayan kimanin makwanni uku sai wasu mutane suka tare ni a masallaci bayan Sallar Azahar, sun zo unguwarmu ne da taimakon dan Sarkin Idi-Araba, wanda ke aiki tare da su, suka ce na shiga mota ni suke nema. Sai na bi su muka je ofishinsu, nan take ya bukaci na je asibiti na karbo bayanin kudin da ake bukata domin a yi mani aikin kafar. Bayan ya yi mini ’yan tambayoyi, na kuma shaida masa a halin da nake ciki, Naira dubu 200 da jama’a suka tara min sun kare a sayen magani da abinci. Sai yac e zai dauki nauyin aikin. Koda na je asibitin kashi na Jami’ar Legas sai suka rubuta mini kudi Naira dubu 613. Da na komo sai jami’an asibitin suka gane da sunan masana’anta za a biya min kudin, sai suka ce ai sun yi kuskure. Nan fa suka kara adadin kudin ya koma Naira dubu 748 da dari 8. Koda na koma na shaida masa haka sai ya ce ya riga ya rubuta Naira dubu 613 kuma ya daukin nauyin biyan kudin. Sauran abin da ya rage Naira dubu 135 da Naira dari 8 za mu nemi taimakon jama’a kuma in Allah Ya yarda zuwa karshen watan nan za a yi mi        ni aikin.” Inji shi.
Wakilan mutumin da ya dauki aikin da su ma suka so a sakaye sunayensu, sun shaida wa Aminiya cewa mutumin ba ya bukatar a ambaci sunansa domin ya yi taimakon ne saboda Allah kuma yana gudun kada riya ta shiga. Sun kuma kara da cewa kuskure aka samu wajan kididdigar kudin aikin kafar. “Domin sai da suka koma wa bawan Allah har a karo na biyu ana samun karin kudin, abin da ya sa suka tsaya a haka kuma su ma ’yan uwan majinyacin sun ce za su cika ragowar Naira dubu 135 da dari 8.” Inji su.