‘Yan sanda sun kama mutum 17 da ake zarginsu da laifukan fashi da kuma kungiyar asiri a sassa daban-daban na Jihar Binuwai.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mukaddas Garba ya gabatar da su a garin Makurdi, inda ya ce daga cikinsu akwai ‘yan asalin Jihar Nasarawa da Filato dsa suka yaudari wani dan acaba zuwa wani otel suka ba shi maganin barci suka gudu da babur dinsa.
An kuma kama wasu ‘yan fashi da suka shiga wani gida a unguwar GRA ta garin Makurdi, suka kwace wayayoyin hannu kirar Iphone 11 Promax da infinix; da jikar agoguna; sa’annan suka yi amfani da wayar suka tura miliyan daya cikin asusun wuru-wuru da suka bude don karkatar da kudin.
Ya kara da cewa, a lokacin binciken an samu wadanda ake zargin da ke zaune a wurare daban-daban da kayan.
Daga cikin abubuwan da aka samu hannunsu, kamar yadda ya gabatar, akwai kudi N300,000 da wayar hannu kirar Iphone 11 Promax da kuma jikar agogunan da aka sace wa mai gidan.
Daga cikin mutanen da aka gabatar akwai wani da ke unguwar Wadata, Makurdi da aka kama bisa zargin fashi da makami.
Kwamishinan ya ce an samu talabijin (plasma) da De-Tech recorder da igiyar yawo ta lantarki da sauran kayayyakin da aka sace a inda aka yi fashin.
Kwamishinan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin fashi da makamin kuma za a kai shi kotu ta yanke masa hukuncin da ya dace da shi.