Kwamitin shirya gasar kwallon kafa ta Sifen ya dakatar da Kocin kungiyar kwallon kata ta Real Madrid na matasa da aka fi sani da Castilla Zinedine Zidane har tsawon watanni uku saboda rashin mallakar sahihin satifiket na horar da ’yan kwallo a gasar rukuni-rukuni a Sifen.
Kwamitin ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan da ya samu koke daga kungiyar masu horar da kwallo ta Sifen inda suka nuna Kocin ba shi da takardun da suka kamata ya zama koci wacce Hukumar shirya wasanni a Turai (UEFA) ta amince.
Shi dai Zidane rahoton ya ce ya mallaki takardar horarwa ce mai mataki na biyu yayin da kwamitin shirya kwallo na Sifen kuma ya ce sai wanda ya mallaki satifiket mai mataki na uku ne kawai ya cancanci ya horar a gasar rukuni-rukuni na kasar don haka Zinedine Zidane bai cancanta ya horar ba, al’amarin da ya sa ta dakatar da shi har na tsawon watanni uku.
Sai dai kulob din Real Madrid na Castillas ya ce zai daukaka kara a kan dakatarwar da aka yi wa kocin nata. Kulob din ya ce yana da shaidar tuni kocin ya mallaki satifiket din horarwa wanda ya yi a kasar haihuwarsa watau Faransa.