Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa, sa’o’i bayan an kai wa jirginta harin bom din nakiya.
Hukumar ta dauki matakin ne bayan jirginta ya taka nakiya da aka dasa a layin dogo a hanyar Kaduna zuwa Abuja a safiyar Alhamis.
- An kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja harin ‘bom’
- An dage ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu har zuwa 10 ga watan Nuwamba
“Saboda wasu dalilai da suka sha karfinmu an dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa nan take, domin kare lafiyar abokan huldarmu.
“Muna ci gaba da aiki domin daidaita komai, kuma nan gaba za mu sanar da ku da zarar an kammala gyare-gyare,” inji sanarwar da hukumar ta fitar.
Sai dai ba ta bayyana zuwa lokacin da ake sa ran dawowar zirga-zirgar jiragen ba.
– Abin da ya faru –
Gabanin taka nakiyar da jirgin kasa ya yi a safiyar Alhamis, a ranar Laraba da dare mahara sun bude wa wani jirgi wuta da nufin samun direbansa, amma ya tsallake rijiya da baya.
Shi ma tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani, wanda ke hanyarsa ta zuwa Abuja a safiyar ya ce: “Yau (Alhamis) da safe ina hanyata ta tafiya a cikin jirgin kasa, jirign da muke ciki ya taka nakiya, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar layin dogon.
“Saura kadan jirgin kasan ya sauka daga kan layin dogo, Allah ne kawai Ya kiyaye.”
Wakilin Aminiya da ke cikin jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna a safiyar Alhamis ya ce fasinjojin jirgin da ya baro Kaduna sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da suke ciki ya taka nakiyar da su.
Ya ce matafiya a jirgin kasa sun yi cirko-cirko a safiyar Alhamis bayan tashin nakiyar a lokacin da jirginsu da ya taso daga Kaduna ya bi ta kan nakiyar.
Daga baya jirgin ya samu karasawa zuwa Abuja bayan an sauya masa layi, amma jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna ba zai iya wucewa, sai dai jan shi aka yi ya koma.