Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da Mai martaba Sarkin Pindiga da ke karamar hukumar Akko, Alhaji Adamu Haruna Yakubu daga sarautarsa, bisa abin da ta kira yawan koke-koken da aka samu daga al’ummar masarautar kan yadda yake tafiyar da al’amuran mulkinsa da kuma zarginsa da wasu laifuffuka.
An dakatar da Sarkin ne a yammacin ranar Talatar da ta gabata, inda gwamnatin jihar ta ce ta nada
kwamitin da zai binciki Sarkin kan irin wannan zarge-zarge da ake yi masa.
Sakon dakatar da Sarkin na Pindiga yana kunshe ne a wata takarda dauke da sanya hannun Babban Sakataren Harkokin Siyasa da Masarautu na Jihar Alhaji Sani A. Kawuwa.
Takardar ta umarci Sarkin ya fice daga ofishinsa nan take don ya ba kwamitin damar gudanar da bincikensa ba tare da yi masa shisshigi ba.
An dakatar da Sarkin Pindiga
Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da Mai martaba Sarkin Pindiga da ke karamar hukumar Akko, Alhaji Adamu Haruna Yakubu daga sarautarsa, bisa abin da ta…
