✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Lalong daga raba masarautar Gbong Gwom Jos

Babbar  Kotun Jihar  Filato ta bai wa Gwamnan Jihar  Barista Simon Lalong umarnin  ya dakatar da raba masarautar Gbong Gwom Jos har ya zuwa lokacin…

Babbar  Kotun Jihar  Filato ta bai wa Gwamnan Jihar  Barista Simon Lalong umarnin  ya dakatar da raba masarautar Gbong Gwom Jos har ya zuwa lokacin da za ta kammala sauraron karar da wasu ’yan kabilar Birom suka shigar a gabanta, kan wannan al’amari.

Mai shari’a Christine Dabup ta kotun ce ta bayar da wannan umarni, bayan da ta saurari karar gwamnatin Jihar Filato  da Lauyan ’yan kabilar Birom Niri Darong ya gabatar a gaban kotun kan wannan al’amari.

Tun da farko dai gwamnatin ta Jihar Filato ta kirkiro masarautu biyu,  masu dajara ta daya a masarautar ta Gbong Gwom Jos wadda ta kunshi kananan hukumomi  hudu.

Daga baya kuma gwamnatin ta bayar da sanarwar Attah Aten na Ganawuri  ne zai zama babban sarki a Karamar Hukumar Barikin Ladi. A yayin da Ujah na Anaguta zai zama babban sarki a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Masu karar mutum bakwai ’yan kabilar Birom  da suka fito daga  gundumomin kibilar Birom na kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Riyom da Barikin Ladi  karkashin jagorancin Daniel Choji sun ruga wannan kotun ne, domin ta dakatar da wannan kuduri na gwamnatin Jihar Filato.

Wadanda ake karar sun hada da gwamnatin Jihar Filato da Babban Mai Shari’a na jihar da Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar.

Sauran su ne shugabannin kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Riyom.

Mai Shari’a Dabup ta yi bayanin cewa ta bayar da wannan umarni ne a ranar 22 ga watan mayu, bayan wani  Daniel Choji ya gabatar da wannan kara, a madadin ’yan kabilar Birom.  Kuma ya roki kotun ta dauki wannan mataki.

Mai karar ya bukaci a dakatar da dukkan wadanda yake kara daga yin wani abu, da zai taba kujejarar masarautar  Gbong Gwom Jos, har ya zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar da ya shigar.

Mai shari’a Dabup ta sanya ranar 11 ga watan Yuli mai zuwa, domin ci gaba da sauraron wannan kara.