Masarautar Egba da ke Jihar Ogun ta dakatar da Olu na Owode da ke Karamar Hukumar Obafemi/Owode, Oba Kolawole Sowemimo, saboda wulakanta takardun Naira.
Majalisar Masarautar Egba, karkashin jagorancin Alake na Kasar Egba, ta dakatar da Olu na Owode daga sarauta ne bayan da wani bidiyonsa ya karade gari, wanda a ciki yake yi wa wani mawaki liki da takardun Naira a wurin wani biki.
A cikin bidiyon kuma, an ga basaraken da wata igiya da aka hada da takardun Naira 1,000, ya nada wa fitaccen mawakin kasar yarbawa, Wasiu Ayinde, wanda aka fi sani da KWAM 1.
A watan da ya gabata ne Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta rubuta wa basaraken wasika cewa ce abin da ya yi zai iya sa a daure shi.
A ranar Juma’a kuma Majalisar Masarautar Egba ta sanar da dakatar da shi kan cin mutuncin kudin Najeriya a bainar jama’a, wanda laifi ne a doka.
Majalisar ta dakatar da shi na tsawon watanni biyu ba tare da albashi ba, bayan shawarar kwamitinta na da’a wanda ya bayyana cewa a tsawon wa’adin dakatarwar, an haramta masa gabatar da kansa a matsayin basarake.
“Da aka tambaye ni ko akwai wani abu da zan ce, sai na mike na ba da hakuri kan duk abin da na aikata ba daidai ba, kuma dakatarwar da aka ce za ta yi na tsawon watanni uku ba tare da albashi ba ta koma wata biyu.
“Na amince da hukuncin da aka yanke.“