Gwamnatin Jihar Ebonyi ta dakatar da Babban Sakataren Ma’aikatar Lantarki da Makamashi na Jihar, Mista Godwin Nwankwo, kan zargin satar man dizel da aka tanada don amfanin fitilun kan titi.
Kazalika, dakatawar ta shafi Hadimi na Musamman ga gwamnan jihar, Mista Emmanuel Nwangbo.
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Atiku ya ce ’yan Arewa su zabi dan uwansu?
- An yi wa dalibai 8,000 karin alawus din karatu a Nasarawa
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Uchenna Orji ne ya shaida wa manema labarai haka jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwar jihar ranar Laraba.
Ya ce, “Majalisar ta amince da dakatar da jami’an biyu wadanda aikin kula da fitilun kan titi ke karkashin kulawarsa.”
Ya kara da cewa, Majalisar ta sami rahoton sace-sacen dizel da ake tafkawa karkashin masu kula da fitilun hanya.
Don haka ya ce, ta ta amince a gudanar da bincike kan badakalar ta hannun hukumar tsaro ta DSS domin gano wadanda ke da hannu a cikin sace-sacen.