An dakatar da wani ɗan kallo shiga filin wasa saboda ihun wariyar launin fata da ya yi wa ɗan wasan Liverpool, Mohammed Salah.
Joel Barwise ya ɗaga murya yana kalaman cin zarafi a lokacin da aka kira sunan Salah a Anfield ranar 21 ga watan Oktoba, kafin wasan hamayya da Everton.
- Tinubu ya gana da gwamnoni kan kuncin rayuwa
- Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da Najeriya —Aminu Dantata
Haka kuma Barwise mai goyon bayan Everton ya yi alamar cin zarafi da yatsarsa kan hadarin da ya faru a filin wasa na Heysel.
Kimanin mutun 39 suka mutu a wani turmutsitsin da ya faru kafin fara Gasar Zakarun Turai wato European Cup a 1985.
Wata kotun majistire a Sefton ce ta yanke hukuncin dakatar da Barwise shekara uku daga shiga kallon tamaula.
Haka kuma an ci tarar Barwise na Bentham Drive a Childwall a Liverpool £500.
Masu shigar da kara sun ce an zaƙulo mutumin ne daga dubban ’yan kallo, bayan da daya daga masu kula da shiga fili ya ga Barwise yana cin zarafi.
Tun da farko dai ’yan sandan Merseyside ne suka gano mutumin a na’urar ɗaukan hoton bidiyo ta CCTV daga nan ne suka tsare shi.