Gwamnatin Tarayya ta dage dawo da ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine daga ranar Alhamis zuwa Juma’a.
Kawo yanzu dai babu wani dalili da gwamnatin ta bayar game dage ranar dawo da ’yan Najeriyan da suka makale a Ukriane, wadda Rasha ta far wa da yaki, mako guda yanzu.
- Yadda ake cin zalin daliban Najeriya da suka makale a Ukraine
- ASUU za ta janye yajin aiki ba da jimawa ba —Ngige
A ranar Labara Ma’aiakatar Harkokin Wajen Najeriya ta sanar cewa rukunin farko na ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine bayan barkewar yaki za su iso Najeriya a ranar Alhamis.
Sanarwar da Ma’aikatar da fitar a ta ce gwamnati ta tura jiragen kamfanin Max Air da Air Peace domin kwaso ’yan Najeriya mazauna Ukraine da suka yi kaura zuwa kasashen Poland, Romania da kuma Slovekia bayan barkewar yakin.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan ’yan Najeriyan — kasar sauran ’yan sauran kasashe mazauna Ukraine — sun bukaci gwamnati da ta taimaka ta dawo da su gida, suna masu zargin jami’an Ukraine da fifita ’yan kasarsu a kan iyakar ficewa daga kasar.