Hukumar kula da shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA ta bayar da sanarwar dage kocin kulob din Atletico Madrid da ke Sifen Diego Simone bayan samunsa da laifin yin fada da dan wasan baya a kulob din Real Madrid da ke Sifen Rapheal barane a wasan karshe na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai a ranar Asabar da ta wuce.
A wasan, Real Madrid ce ta lashe kofin bayan ta lallasa ta Atletico Madrid da ci 4-1.
Jim kadan bayan Cristiano Ronaldo ya zura kwallo a ragar Atletico a bugun fanariti ne sai barane ya narka wa kocin kwallo a matsayin murna amma hakan bai yi wa kocin dadi ba al’amarin da ya sanya shi shiga cikin filin wasa don jin dalilin da ya sa dan kwallon Madrid din ya yi masa haka.
Laifin kocin shi ne yadda ya shiga cikin filin wasa ba tare da an tashi ba don haka hukumar ta dage shi tsawon wasanni shida a gasar da za a yi badi idan Allah Ya kaimu yayin da shi kuma barane aka ba shi katin gargadi (Yellow Card).
Da wannan dagewar da aka yi wa kocin ba zai zauna benchi a wasanni shida da kulob din Atletico Madrid zai yi a matakin farko na gasar ba a kakar wasa mai zuwa ba.
An dage kocin Atletico Madrid a wasanni 6
Hukumar kula da shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA ta bayar da sanarwar dage kocin kulob din Atletico Madrid…