✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage filin wasa na Maiduguri saboda matsalar tsaro

Kwamitin da ke shirya gasar rukuni-rukuni na kasa da aka fi sani da League Management Company (LMC) a ranar Juma’ar da ta wuce ne ya…

Kwamitin da ke shirya gasar rukuni-rukuni na kasa da aka fi sani da League Management Company (LMC) a ranar Juma’ar da ta wuce ne ya bayar da sanarar dage filin wasa na Maiduguri daga cigaba da yin wasanni rukuni-rukuni na kasa har sai abin da hali ya yi saboda matsalar tsaro.
Tuni kwamitin ya bayar da sanarwar a kafar sadarwarsa ta Twitter na dage wasa a tsakanin kulob din El-Kanemi Warrior na Maiduguri da na Abia Warriors a wasa karo na biyu zuwa Kano.
Kwamitin ya ce ganin yadda tashe-tashen hankula ke yawan aukuwa a Maiduguri ta sa kulob din Abia Warriors ya nemi da a canja masa filin wasan da za su kara da El-Kanemi Warriors saboda matsalar tabarbarewar tsaro kuma tuni kwamitin ya amince da hakan.
Hasalima dia kwamitin ya yanke shawarar komawa da kulob din El-Kanemi Warriors Kano don cigaba da gudanar da wasanninsa na gida a gasar har zuwa wani lokaci..