Hukumar Kula da Jigilar Jiragen Kasa a Najeriya NRC, ta sanar da dage dawo da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna har sai abin da ya sawwaka.
Wannan na zuwa bayan sanarwar da Hukumar NRC ta fitar a makon nan da ta bayyana cewa za a dawo da zirga-zirgar jirgin a ranar Litinin 23 ga watan Mayu da muke ciki.
- An kama Boka da tawagarsa da ake zargi da kashe ’yar sanda a Imo
- Majalisar Yobe ta yi fatali da batun tsige Gwamna Buni
Sanarwar da Kakakin NRC, Mahmood Yakub ya fitar a Yammacin ranar Juma’a, ya ce za a sanar da sabuwar ranar dawo da zirga-zirgar nan ba da jimawa ba.
Ana dai ganin cewa dage dawo da zirga-zirgar na da nasaba ne da cimma muradin ’yan uwan wadanda aka sace yayin harin da aka kaiwa jirgin kasan a ranar 28 ga watan Maris na bana.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan uwan wadanda harin ya rutsa da su sun bukaci Gwamnatin Tarayya a kan kada ta dawo da zirga-zirgar jirgin kasan har sai an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a sakamakon harin.
A kan haka ne dai gwamnatin take sake tabbatar wa iyalan fasinjojin jirgin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su cewa ta dauki batun kubutar da su da matukar muhimmanci;
Fiye da kwanaki 40 ne ’yan bindiga suka dasa bom a kan titin jirgin kasan Kaduna-Abuja yayin da suka kai wa jirgin kasan hari, inda suka kashe fasinja 10, suka sace akalla 60, tare da jikkata wasu da dama.
A cewar gwamnatin, tana aiki ka’in da na’in domin ganin an sako fasinjojin ba tare da komai ya same su ba, amma ta ki yin karin bayani saboda abin da ta kari ‘muhimman dalilan tsaro’.
NRC ta bai wa matafiya tabbacin samun karin tsaro a hanya da kuma cikin jirgin, “Ba wai ga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba kawai, har ga daukacin fasinojojin jirign kasa,” inji sanarwar da Yakub ya fitar.