An dage wani dan kwallo mai suna Ricardo Ferreira dan wasan baya a kulob din Futebol Clube da ke kasar Suwizilan daga yin kwallo har na tsawon shekara 50 bayan an same shi da laifin yaba wa alkalin wasa kwallo a fuska sannan kuma ya antaya masa ruwa da hakan ya sa alkalin wasan ya jike sharkaf yayin da wasa ke gudana. dan kwallon ya yi haka ne saboda rashin gamsuwa da yadda alkalin wasan yake yi musu alkalanci.
Shi dai dan kwallon, an taba dage shi daga yin wasanni 45 a baya, bayan an same shi da laifin cin zarafin takwarorinsa a lokacin da wasa ke gudana. Sai dai ya bayyana tsananin kaduwarsa da wannan hukunci da Hukumar shirya kwallon kafa ta kasar ta kakaba masa na dage shi daga yin wasa har na tsawon shekara 50.
dan shekara 28, Ricardo an shaide shi da dan kwallon da ya fi kowane nuna rashin da’a a gasar rukunin ’yan dagaji (amateur) ta kasar don da wuya ya yi wasa ba tare da ya janyo abin da zai sa a dage shi ta hanyar ba shi katin kora (red card) a lokacin da wasa ke gudana ba. Da abin ya yi yawa ne ya sa Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta kasar ta dauki wannan mataki a kansa a wannan karo don ya zama darasi ga saura.
“Ban taba tunani za a dage ni daga yin wasanni har na tsawon shekaru 50 ba, ni a zatona bai fi a dage ni a tsawon shekaru biyu ko uku ba”, inji dan kwallon a lokacin da yake nuna takaicinsa ga menama labarai.
Shi ma Lauyan gasar rukunin ’yan dagaji na kasar Suwizilan Robert Breiter ya bayyana bacin ransa a kan yadda ake samun yawan dage ’yan kwallo a gasar, al’amarin da ya ce ya yi maraba da dagewar da aka yi wa Riarcdo Ferriera daga yin kwallo har na tsawon shekara 50 kuma hakan zai sa masu yunkurin aikata irin haka su shiga taitayinsu.
Wannan dagewar da aka yi wa Ricardo ta sa ba zai sake buga kwallo ba har sai ya kai shekara 78 idan Allah Ya yi masa tsawon kwana.