Jami’an tsaron farin kaya na DSS sun yi awon gaba da jagoran haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da shari’arsa.
Kotun dai wacce Kanun ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis ta dage ci gaba da sauraron karar wacce Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa har zuwa 10 ga watan Nuwamban 2021.
- Mawakin da ya yi mutuwar karya a Ghana ya shiga hannu
- BUK za ta fara yin takin zamani da iskar gas daga dagwalon masana’antun fata
Gwamnatin dai na zarginsa dai aikata laifuka bakwai da ke da alaka da cin amanar kasa da ta’addanci da yunkurin tayar da zaune tsaye.
Sai dai ya musanta aikata dukkan laifukan da ake zarginsa da su.
Yayin zaman kotun na ranar Alhamis dai, sai da lauyoyinsa, Ifeanyi Ejiofor suka bukaci a basu belin wanda suke karewa amma kotun ta ki.
Daga nan ne kuma ak yi awon gaba da shi a wasu ayarin motoci Hilux.
Tun da farko dai babban lauyan Kanun, Ifeanyi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kawo wanda yake karewa a kotun.
A cewar lauyan, wanda ya nemi bukatar yayin wani taron manema labarai Abuja ranar Laraba, tun da dai Babban Jami’i mai shigar da kara na GwamnatinnTarayya ya shigar da sabbin tuhumce-tuhumce har guda bakwai a kan Kanun, bai ga dalilin da zai sa a hana shi bayyana a kotun ba.
Ya yi korafin cewa bayan gwamnati ta gurfanar da wanda yake karewa ba tare da masaniyar lauyoyinsa ba a ranar 29 ga watan Yuni, ta kuma gaza kawo shi kotun ranar 26 ga watan Yuli lokacin da bukatar hakan ta taso.
Ya ce hakan dai ya saba umarnin kotun wacce Mai Shari’a Binta Murtala Nyako ta bayar.
A ranar Litinin, 18 ga watan Oktoban 2021, Gwamnatin Tarayya ta shigar da sabbin tuhumce-tuhumce a kan Kanun mai kunshe da zarge-zarge har guda bakwai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Yayin zaman kotun na ranar Alhamis dai, Aminiya ta ga yadda aka girke tarin jami’an tsaro na ’yan sanda da na DSS a dukkan kofofin shiga kotun.