Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta bayar da sanarwar dage alkalin wasan da ya yi allakanci a wasan da Tunisiya ta yi da Ekuatorial Guinea a matakin kwata-fainal bayan ya ba Ekuatorial Guinea bugun fanariti ana gab da tashi da hakan ya sa aka fitar da Tunisiya da ci 2-1 a gasar.
Alkalin mai suna Rajindraparsad Seehurn ya fito ne daga kasar Mauritiaus.
Jim kadan bayan an tashi wasan ne magoya bayan Tunsiya da wasu daga cikin ’yan kwallon suka harzuka kuma suka nemi lakadawa alkalin wasan duka har sai da jami’an tsaro suka kubutar da shi da kyar da jibin goshi.
Bayan Hukumar CAF ta yi nazarin wasan ne, sai ta gano bai kamata a ce alkalin wasan ya ba Ekuauatorial Guinea bugun fanariti a wasan ba.
A ranar Talatar da ta wuce sai Hukumar CAF ta bayar da sanarwar ta dage alkalin daga yin alkalanci har na tsawon watanni shida a matakin farko sannan akwai yiwuwar ta sake daukar wani mataki a kansa a bisa kuskuren da ya yi a lokacin da ya yi alkalancin wasan.
A bangaren Tunisiya kuwa, Hukumar CAF ta ci ta tarar Dala dubu 50 kwatankwacin Naira miliyan 10 da dubu 350 ne saboda yadda magoya bayan Tunisiya da wasu daga cikin ’yan kwallonta ska yi barna a filin wasan saboda harzukar da suka yi. Sai dai CAF ta ce babu yiwuwar cin tarar wasu daga cikin ’yan kwallon da suka yi barnar, al’amarin zai tsaya ne a kan kasar kawai, ba tare da an hukunta wani ko wasu daga cikin ’yan kwallon ba.
Hasalima, hakan ce ta sa Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa a Tunisiya ya yi murabus daga Hukumar CAF akan abin da ya kira yi wa kasarsa magudi a gasar a ranar Litinin da ta wuce a wata sanarwa da Tunisiya ta fitar..