✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dade a na barazana ga raina – Malamin da aka harba a Abuja

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu mutane da ba a san su wane ne ba suka yi yunkurin halaka wani malamin addinin Musulunci…

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu mutane da ba a san su wane ne ba suka yi yunkurin halaka wani malamin addinin Musulunci mai suna Malam Aliyu Abubakar dan Aliya a garin Kubwa da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja inda wani mutum ya harbe shi da bindiga a lokacin da yake komawa gida. Wakilinmu ya tattauna da shi a gadonsa na asibiti kan yadda lamarin ya faru:

Aminiya: Ko za ka tuna yadda wannan al’amari ya faru da kai?
Malam dan Aliya: Kamar karfe tara da ’yan mintoci na dare, bayan dawowata daga gida Sakkwato a ranar Asabar da ta gabata, Ahmad Tijjani wanda abokina ne, ya raka ni garin Mpape a nan karamar Hukumar Bwari na kai wani sako. Bayan mun yi Sallar Magariba, mun wuce zuwa yankin Maitama inda gidan uwargidana yake, sannan ya dauko ni zuwa Kubwa a kan hanyata ta zuwa gidan amaryata. Mun tsaya a daidai wata mashigar Kubwa daga kan babban titin zuwa Abuja a kusa da kwanar Hukumar NYSC kafin na fito daga mota, sai kawai na ji an ja kofar an bude, wani mutum ya nemi jawo ni waje, amma Allah bai ba shi nasara ba, a lokacin na gane raina suke nema ba mota ko kudi ba. Nan take na ja kofar na rufe, shi kuma abokina da ke tuka motar sai ya ja ta cikin hanzari moka juya zuwa ta hanyar zuwa cikin gari. Haka ke da wuya sai ga karar bindiga an harbe ni a kafada ta daga nan kuma muka taho zuwa nan asibitin inda aka yi mini aiki a wurare uku da ya hada da kafadata da kirji da ciki saboda saboda kwararar jini ta cikin cikina.
Sama da shekara biyu ke nan wani na kirana ta waya lambarsa a boye, akwai lokacin da ya kira ni sama da awa daya amma bai yi magana ba, sai kuma wani sakon waya da ke cewa sai ya ga bayan rayuwata, to ina zaton wadannan ne suka nemi cika burinsu a yanzu.
Aminiya: Ko ka sanar da hukuma kan barazanar a wancan lokaci?
Malam dan Aliya: Na sanar da hukuma a lokacin bayan da na samu sakon, na kuma kai korafi ne a babban ofishin ’yan sanda na Kubwa inda suka ce za su je kamfanin sadarwa don karbar lambar tare da bincike a kai. Sai dai har zancen nan da muke yi ba su yi komai a kai ba, in ban da yaudarata da suka yi ta yi sannan suka amshi kudi a wurina da sunan za su yi bincike.
Aminiya: Me kake ji ya sa mutanen suke neman rayuwarka?
Malam dan Aliya: Ba ko mai ba ne ya sa suke yi mana azaba ba, sai dai kawai saboda mun yii imani da Allah Mabuwayi abin godiya. Saboda haka a kan addini ne kawai, ni ba dan kasuwa ba ne, kuma ban da wata adawa a tsakanina da kowa, iyakata karantar da addini. Sai dai koda an kashe mu akwai wadanda muka yaye da za su dora daga inda muka tsaya.
Aminiya: To su wadanne irin mutane ne kake ji?
Malam dan Aliya: Abu guda dai da ya bayyana mutanen nan ba Hausawa ba ne, kuma ba ma ’yan Arewa ba ne, suna magana ne da Turanci irin na burokin. Kuma bayanin da na samu daga bisani shi ne an ga wata farar mota da ta tsaya ta bayanmu, a inda muka tsaya a Mpape, sannan an ga ta tashi bayan mun bar garin.
Aminiya: Me za ka ce a kan wannan al’amari?
Malam dan Aliya: Bayanina shi ne, shi dai addini ba za mu daina karaantar da shi ba, rayuwata na hannun Allah ne, kuma rai ba za ta mutu ba sai da izinin Allah ta hanyar ajali da Ya sabbaba wa bawanSa.