✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cinna wa gidan Sunday Igboho wuta

Kakakin ’yan sandan Jihar Oyo ya tabbatar wa da Aminiya hakan a safiyar Talata.

Rundunar ’yan Sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kone gidan mai rajin kafa kasar Oduduwa, Cif Sunday Igboho da wasu bata gari suka yi a ranar Talata.

Kakakin ’yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan.

“A safiyar Talata ne ofishin ’yan sanda na Santo ya samu rahoton wasu bata gari sun cinna wa gidan Sunday Igboho wuta a unguwar Soka da ke a garin Ibadan.

“Bata garin sun dauki tsawon lokaci suna harbi a iska kafin su suka cinna wa gidan Igboho wuta,” inji Fadeyi.

Bayan samun rahoton faruwar lamarin shugaban ’yan sandan caji ofis din da ke Santo, ya tuntubi Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, wanda nan take suka garzaya yankin.

Daga bisani ana samu nasarar kashe wutar, amma ta yi barna sosai a gidan.

Kakakin ’yan sandan ya ce jami’an ’yan sanda sun baza komarsu don kama wanda suka aikata hakan.

%d bloggers like this: