Hukumar Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta ci gidan radiyon Nigeria Info tarar Naira miliyan biyar bisa laifin watsa maganar da tsohon mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Obadiah Mailaifa.
Kwanakin da suka gabata, Mailafiya a wata hira da ya yi da tashar, ya ce wani gwamna mai ci a Arewacin Najeriya ne Shugban Boko Haram a Najeriya.
Tuni ya amsa gayyatar da hukumar tsaro ta DSS inda ya amsa tambayoyi na akalla awa shidda. Daga baya wasu kafafe (ba Aminiya ba) sun ruwaito shi yana cewa an yi wa maganarsa gurguwar fahimta.
Hukumar NBC ta bayyana cin tarar gidan radiyon ne a takardar da ta fitar mai dauke da sa hannu shugabanta, mai taken ‘Hukumar Watsa Labarai ta ci tarar Nigeria Info 99.3 kan karya dokar watsa labarai’.
Aminiya ta ruwaito kwanakin baya cewar NBC ta kara yawan tarar karya dokar watsa labarai daga N500,000 zuwa miliyan biyar.
A lokacin tattaunawarsa da gidan radiyon, Mailafiya ya yi magana a kan kashe-kashen da ake yi a Kudancin Kaduna da ta’assar ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.
“Wasu daga cikinmu muna da bayanan sirri. Na hadu da wasu yan bindiga; mun hadu da manyan kwamandojin ‘yan bindiga – daya ko biyu da suka tuba sun zauna da mu ba so daya ba, ba sau biyu ba.
“Sun gaya mana cewar wani gwamna a jihohin Arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.
“Boko Haram da ‘yan bindiga duk abu daya ne. Suna da makaman zamani. Ko lokacin da aka kulle jihohi jiragensu na yawo.
“Suna yawo da makamai da kudi suna rabawa a bangarori daban-daban na kasar nan”, inji Mailafiya.
NBC dai ta ci tarar gidan radiyon ne kan bayar da kafar da ya yada bayanan da ka iya kawo cece-ku-ce har ma da miyagun laifuka da tayar da zaune tsaye.