✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ci gaba da sauraron shari’ar ‘bidiyon Dala’ na Ganduje

Bangaren Ganduje sun kawo karin sabbin lauyoyi domin kare shi.

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Titin Miller na Unguwar Bompai, ta ci gaba da sauraron shari’ar bidiyon sunkuma daloli a cikin aljihu da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana yi.

A shekarar 2018 ne aka wallafa bidiyon zargin Ganduje yana sanya daloli a cikin aljihu wanda ake zargin cin hanci ne daga wani dan kwangila a Jihar, sai dai makarraban gwamnan suka ce bidiyon na bogi ne kuma an yi hakan ne don a bata wa gwamnatin suna.

Sai dai mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar wanda ya fitar da bidiyon ya dage a kan cewa sun inganta kuma babu coge a cikinsu.

A yayin zaman kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Sulaiman Baba Na Malam, a ranar Litinin, lauyan Jaafar Jaafar da na jaridar Penlight sun soki yadda masu wakiltar bangaren Ganduje suka kawo sabbin lauyoyi sabanin wadanda aka fara shari’ar da su tun fil azal.

Aminiya ta samu cewa, Mai Shari’a Na Malam ya yi watsi da sukar lauyoyin masu karar suka yi, inda kuma ya sake dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Afrilun 2021.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom mai tushe a Kanon Dabo ya ruwaito, ya ce lauyoyin Gwamna Ganduje sun ce ba sababbin lauyoyi suka kawo ba, illa iyaka kari ne a kan lauyoyin da suke kare su.

Shi kuwa lauyan Jaafar Jaafar, U. U Ete cewa ya yi, sun yi sukar ne ganin yadda aka zo da sabbin fuskoki a madadin Barista Nura Ayagi da aka fara shari’ar da shi tun usuli.